Najeriya ta ƙarfafa ƙawancen tsaronta da Amurka

Najeriya ta Amuka sun amince da ƙarfafa haɗin kan tsaro tsakaninsu domin yaƙi da ta’addanci. Cikin wata sanarwa da kakain shugaban ƙasar Bayo Onanuga ya fitar, ya ce an cimma hakan ne a ganawar da mai taimaka wa shugaban ƙasar kan harkokin tsaro Mallam Nuhu Ribadu ya yi da mataimakin shugaban Amurka, JD Vance da […]

Read more

EFCC ta ayyana neman Sadiya Farouq ruwa a jallo

Hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta ayyana neman tsohowar ministar jin ƙai ta ƙasar, Sadiya Umar Farouq ruwa a jallo. Cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na internet, ta ce tana neman tsohuwar ministar bisa zarge-zargen laifukan haɗa baki domin aikata laifuka da amfani da ofishi […]

Read more

Jam’iyyar NDC na gudanar da babban taronta na ƙasa

Jam’iyyar hamayyar ta NDC a Najeriya na gudanar da babban taronta na ƙasa domin zaɓen sabbin shugabanninta. Matakin na zuwa ne mako guda bayan da manyan jiga-jigan siyasar ƙasar biyu, Peter Obi da Kwankwaso suka sanar da komawa cikinta. Ɗaruruwan magoya bayan jam’iyyar ne suka taru a harabar wurin gudanar da taron a Abuja. Akwai […]

Read more

Hisba ta kama mutane 7 dake musayar matansu na aure

Hukumar Hisba a shiyyar Katagum ta jihar Bauchi ta yi nasarar kama wasu mutane bakwai da ake zargi da aikata wani sabon salo na musayar mata domin hulɗar aure da jima’i a tsakanin su, a Azare cikin ƙaramar hukumar Katagum. Bayanan hakan ya fito ne daga bakin Kwamandan Hisba na shiyyar Katagum, Malam Ridwan Muhammad […]

Read more