Gwamnatin Najeriya ta sha alwashin ƙarfafa dakarun ƙasar

Gwamnatin Najeriya ta alƙawarta sake ƙarfafa dakarun tsaron ƙasar domin magance matsalar tsaro da ke addabar wasu sassan ƙasar. Mataimakin Shugaban Ƙasar, Kashim Shettima ne ya bayyana haka a lokacin taron addu’o’i na musamman ga dakarun tsaron ƙasar da aka gudanar a Babban Masallacin Juma’a na ƙasa da ke Abuja, babban birnin ƙasar. Shettima ya […]

Read more

Kungiyar SHUDLAS tare da kamfanin Moving Image sun kudiri aniyar ci gaba da wayar da kan mutane illar cin hanci.

An bukaci jama’a da kungiyoyin al’umma su dinga bibiyar aiyukan da gwamnatoci ke sanyawa cikin kasafin kudinsu na kowacce shekara, domin samun daidaito da kuma kaucewa al’mundahana yayin gudanar da aiyukan. Kungiyar masu sauraren shirin wasan kwikwayon, Shugabanci, SHUDLAS wanda kamfanin Moving Image ke gabatarwa ne suka shirya taron, tare da gabatar da makaloli daga […]

Read more

AFCON 2025: Nijeriya ta kora Aljeriya gida

Tawagar ƙwallon ƙafa ta Najeriya, Super Eagles ta lallasa abokiyar hamayyarta, Aljeriya da ci biyu da babu a wasan kwata fainal da suka buga na Gasar AFCON ta 2025. Yanzu Nijeriya ta tsallaka matakin wasan kusa da na ƙarshe, bayan samun nasara da yammacin ranar Asabar. Victor Osimhen ne ya fara jefa ƙwallo a ragar […]

Read more

Yajin Aiki: NARD Za Ta Yi Zanga-Zangar Lumana A Zariya

Ƙungiyar Likitoci Masu Sanin Makamar Aiki ta Najeriya (NARD), reshen Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello (ABUTH) da ke Zariya, ta sanar da aniyarta ta shiga yajin aiki na ƙasa da aka shirya fara wa a ranar 12 ga watan Janairu, 2027. Wannan ya biyo bayan gazawar Gwamnatin Tarayya wajen cika yarjejeniyar da ta cimma […]

Read more

Na Gamsu Ana Kashe Musulmai A Najeriya — Trump

A karon farko tun bayan da ya fara magana kan matsalar tsaro a Najeriya, Shugaban Amurka, Donald Trump, ya amince cewa ana kashe Musulmai a ƙasar. A baya, Trump ya sha bayyana cewa hare-haren da ake kai wa a Najeriya sun fi shafar Kiristoci kaɗai, duk da cewa rahotannin sun nuna cewar mutane daga kowane […]

Read more