‘Yan bindiga masu garkuwa da mutane sun sace Mai Anguwan Babangida a masarautar Kauru, Malam Babangida Sogiji da wasu mutane 11 a wasu tagwayen hare-hare da aka kai a kauyukan Libere da Unguwan Babangida a karamar hukumar Kauru ta jihar Kaduna.
Aminu Khalid shugaban matasan yankin Dokan Karji ya shaida wa jaridar daily trust cewa, mutane hudu da aka yi garkuwa da su, an sace su ne da tsakar ranar Alhamis a lokacin da suke girbiva gonakinsu.
“Bayan harin ranar Alhamis, ‘yan bindigar sun koma Unguwan Babangida da safiyar Juma’a, inda suka yi awon gaba da wasu mutane shida, ciki har da mai anguwa,”
- Gwamnatin Jihar Kano Ta Ƙuduri Aniyar Farfaɗo Makarantun Kimiya Da Fasaha
- An Dakatar Da Mamman Osuman Daga Shugabancin ACF
Ya kara da cewa biyu daga cikin mutanen da aka sace ‘yan cirani daga jihar Jigawa da suka zo yankin domin aikin noma.
“Har yanzu muna jiran ‘yan bindigar su tuntube mu domin neman kudin fansa ko tattaunawa,”
Khalid ya bayyana damuwarsa kan tabarbarewar tsaro, inda ya ce lamarin ya haifar da firgici a yankin na Libere da kewaye, lamarin da ya tilastawa mazauna yankin tserewa.
“‘Yan bindiga sun mamaye wasu kauyuka a karamar hukumarmu ba tare da fuskantar kalubale ba, suna yin abin da suka ga daban-daban,”
Duk ƙokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, Mansir Hassan, ya ci tura, domin bai amsa kiran da aka yi masa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.