An yi jana’izar mahaifiyar tsohon shugaban hukumar shigi da fici ta Najeriya kuma mamallakin tashoshin FM da Radio na MUHASA Muhammad Babandede a masallacin Zhera in da aka binne ta a makabartar Gandu dake Kano.
Allah ya yiwa Hajiya Hajara wacce akafi sani da Hajiya Uwani rasuwa, a ranar Alhamis 26 Disamba, 2024.
Hajiya Hajara (Uwani) ta rasu tanada shekara 90 ta bar yaya biyu: Hajiya Yelwa da kuma Alh Muhammad Babandede. A kididdiga an ce Hajiya Hajara ta bar sama da 70.
Manyan baki daga ciki da wajen Najeriya sun halarci jana’izar Hajiya Hajara, inda mataimakin shugaban ma’ikatan fadar gwamntin Najeriya Sanata Ibrahim Hassan Hadejia ya wakilci mataimkain shugaban kasa Kashim Ibrahim Shettima.
Sai kuma Sanata Uk Umar, Durbin Rano kuma tsohon shugaban hukumar shigi da fici ta Najeriya wanda ke matsayin siriki ga Alhaji Muhammad Babandede.