Al’ummar unguwar Tudun Yola dake karamar hukumar Gwale a jihar Kano, sun tashi da jimamin mutuwar wasu matan aure biyu, da aka zargin wasu batagari ne suka yi musu kisan gilla sannan suka kunna wuta a gidan.
Rahotanni na cewa wadanda ake zargin sun shiga gidan fuskokinsu a rufe, inda suka dibi man fetur, a cikin injin janareta sannan suka kunna Wuta tare da sossokawa matan auren makamai a wasu sassan jikinsu.
Matan da aka halaka, sun hada da Hauwa’u Yakubu da kuma Zahra’u Aliyu, wadanda dukkansu mata ne ga, Alhaji Ashiru Shu’aibu Usaini.
Alhaji Ashiru Shu’aibu Usaini, ya bayyana matukar damuwarsa kan wannan al’amari da ya kasance na kaseh matansa, inda ya yi musu addu’ar Allah ya ji kansu, Allah kuma ya toni asirin wadanda suka aikata kisan ga matan nasa don su fuskanci hukunci
- Nijeriya Ta Doke Gabon A Wasan Neman Tikitin Kofin Duniya
- Majalisar Wakilan Najeriya Ta Nemi A Dage Soma Amfani Da Kwamfuta A Jarrabawar WAEC
Daya daga cikin yaran sa, mai suna Sagir Ashiru, ya bayyana cewa, ana kyautata zaton lamarin ya faru ne da misalign karfe 12 zuwa 1:00pm na ranar Laraba, har zuwa marigaba babu wanda sani har sai da mutanen gidan suka dawo daga kasuwa aka ga kofar a rufe kuma an kiwo wayoyinsu duk a rufe.
Ya kara da cewa bayan mai gidan ya dawo ya shiga ciki sai yaga alamun tashin gobara , sai suka tarar da an kashe su bayan an kunna wuta a gidan baya ga sossoka musu karfe da batagarin suka yi, yayin daya kuma ta yi gudun tsira a bandaki amma ita ma sun yi amfani da ita ce da kuma Tabarma wajen kunna wuta wanda hayakin yayi sanadiyar rasuwarta.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kano CSP Abdullahi Kiyawa, ya bayyana cewa suna kan bincike kan lamarin