Majalisar wakilan Najeriya ta yi kira ga gwamnatin ƙasar ta dakatar da shirin da hukumar shirya jarrabawar kammala sakadire ta WAEC ke yi na soma amfani da kwamfuta a jarrabawar shekarar 2026, inda ta yi gargaɗin za a iya samun dalibai da dama da za su yi rashin nasara.
Hakan ya biyo wani kuduri da ɗan majalisa Kelechi Nworgu ya gabatar, inda ya buƙaci majalisar ta shiga tsakani kan abin da ya ce zai iya zama barazana ga fannin ilimi.
Ya ce duk da dai ana amfani da kwamfuta a jarrabawar JAMB, halin da akasarin makarantun sakandire ke ciki a faɗin kasar ya sa ya ke ganin sauyawa zuwa kwamfuta a jarrabawar 2026 ya yi wuri.
”Da yawa daga cikin makarantu dubu 25,500 da ke ƙasar, musamman na karkara, ba su da naurorin kwamfuta da ke aiki, ko ƙwarrarun malaman koyar da ilimin ƙwanfuta. Da dama daga cikinsu ma ba su taɓa yin amfani da kwamfuta ba, gashi kuma ana ƙoƙarin tilasta musu zana jarrabawar da kwamfuta, in ji shi.
Dan majalisar ya bukaci ma’aikatar ilimi da hukumar shirya jarrabawar ta WAEC su ɗage fara amfani da kwamfuta na tsawon shekaru uku, kafin nan an ɗauki matakan da su ka dace tare da samar da kayayyakin aiki.