Ba Zanje Wajen Babban Taron PDP Ba- Sule Lamido

Tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido ya ce ba ya goyon bayan babban taron jam’iyyarsu ta PDP, kuma ba zai je taron ba saboda nasarar da ya yi a ƙorafin da ya shigar gaban kotu na dakatar da taron.

Lamido ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan kotun tarayya a Abuja ta umarci PDP ta dakatar da shirin taron har sai ta bashi damar yin takarar shugabancin jam’iyyar.

“Na je kotu ne domin ƙwato ‘yancina da jam’iyyata ta ƙwace,” a cewarsa cikin wata hira da kafar Channels TV ranar Juma’a da dare.

Haka nan cikin cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Lamdio ya musanta labarin da ya ce ana yaɗawa cewa ya janye ƙarar tun kafin a yanke hukuncin bayan ganawarsa da gwamnan Oyo kuma wai yana goyon bayan taron.

“Ba zan je taron da kotu ta yi hukunci a kansa ba. Me ya sa zan je? Idan na je taron na yi watsi da nasarar da na samu kenan. Zan yi biyayya ga hukuncin kotun saboda ni mai biyayya ne ga jam’iyya da ya yarda da doka da oda.”

A makonnin da suka gabata ne tsohon gwamnan ya zargi PDP da “juya masa baya” bayan an hana shi sayen tikitin takara domin neman shugaban jam’iyyar a matakin ƙasa, wanda za a gudanar a yau Asabar da Lahadi.

Post masu alaƙa

Kano: Gini Ya Rufta Kan Mutane 16 Ciki Har Da Yara Shida

KACRAN: Babu wani babban rikicin manoma da makiyaya a Yobe

CP Ibrahim Bakori ya kai gaisuwar ban-girma ga Sarkin Karaye tare da halartar bikin rantsar da yan NYSC.