Yadda Babban Taron Jam’iyar PDP Ke Gudana A Oyo

Shugabanni da wakilai da magoya bayan babbar jam’iyyar adawa a Najeriya ta PDP sun yi wa filin wasa na Lekan Salami tsinke domin halartar babban taronta na ƙasa.

Ana gudanar da taron ne a birnin Ibadan na jihar Oyo da ke kudancin ƙasar, kuma jam’iyyar ce ke mulkin jihar ƙarƙashin Gwamna Seyi Makinde.

“Duk wanda ya kamata ya zo wurin nan ya zo, gwamnonimu da sanatoci masu-ci da marasa ci dukkansu suna nan mun hallara a Ibadan,” kamar yadda ɗan kwamatin amintattun PDP Farfesa Umar Tsauri ya shaida wa BBC.

Ana sa ran wakilai kusan 3,000 ne za su kaɗa ƙuri’unsu a yau Asabar zuwa Lahadi domin zaɓen sabon shugabancin jam’iyyar a matakin ƙasa domin maye gurbin na yanzu ƙarƙashin Umar Ilya Damagun.

Sai dai ana gudanar da taron ne bayan umarnin kotu aƙalla biyar daga shari’o’i aƙalla uku da suka ce a yi taro ko kada a yi bisa dalilai daban-daban.

Post masu alaƙa

Dubun masu ƙera muggan makamai a Filato ta cika

Dalilin da ya sa na gina Masallatai 50 da aurar da marayu 10 — Mataimakin Gwamna

Dalilin da ya sa zan yi takara – Yusuf Buhari