Sulhu Da Yan Ta’adda A Katsina Ne Ke Haifar Da Hare-haren Yan Bindiga A Kano- Kwankwaso

Jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce sulhu da ƴanbindiga da wasu al’umomin jihar Katsina ke yi ne ya janyo samun hare-hare a wasu yankunan jihar Kano.

Yayin da yake jawabi a wurin taron yaye ɗalibai na jami’ar skyline da ke Kano, Sanata Kwankwaso ya ce gwamnatin tarayya ce ya kamata ta yi sulhu ba ƙaramar hukuma ba.

Tsohon gwamnan jihar Kanon ya ce ƴan bindiga na shiga Kano daga Katsina su kashe mutane bayan sulhu a wasu ƙananan hukumomi.

”Babu laifin sulhu amma dole gwamnatin tarayya ta sa baki, babu ma’ana ƙaramar hukuma ɗaya ta ɗauki matakin ita kaɗai, dole gwamnatin tarayya ta sa baki”, in ji shi.

Kwankwaso ya kuma yi kira ga shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ƙara mayar da hankali kan matsalar tsaro a faɗin ƙasar.

Dole shugaban ƙasa ya nuna jajircewa a matsayin babban kwamandan hafoshin tsaro.

Post masu alaƙa

2027: Tinubu da Atiku da Obi za su fafata a muhawarar ƴan takarar shugaban ƙasa

2027: NDC ta zargi APC da gwamnatin Kano da shirin yin magudi ta tsarin tattara sakamakon zabe na INEC

Yan sanda sun buƙaci haɗin kan al’umma wajen yaƙi da shaye-shayen miyagun kwayoyi a Kano