Ban yi nadamar goya wa Tinubu baya ba – Wike

Ministan Abuja babban birnin Najeriya ya ce bai yi nadamar goya wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu baya ba tun daga 2022, duk da kasancewarsa ɗan jam’iyyar PDP mai adawa.

Wata sanarwa da mai magana da yawunsa ya fitar, Nyessom Wike ya ce ya ɗauki matakin ne “bisa dacewa da ɗabi’a da kuma aƙidarsa”, yana mai cewa “ban taɓa ɓoye goyon bayana ga Shugaba Tinubu ba tun daga farko”.

Ministan ya bayyana haka ne yayin taron bikin cikarsa shekara 58 da haihuwa yau Asabar a Abuja, wanda ya samu halartar ‘yansiyasa daga jam’iyyu daban-daban.

Wike ya goyi bayan Tinubu ne bayan samun saɓani da shugabannin PDP ana dab da zaɓen 2023, rikicin da ya kai shi ga zama minista a gwamnatin APC wanda kuma har yanzu ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.

Post masu alaƙa

Atiku ya yi zargin ƙoƙarin hana shi takara a 2027 saboda kasancewarsa ɗan Arewa

Ana taƙaddama kan zaɓen fitar da gwanin sanatan Zamfara ta Arewa

Kotu ta daure Saminu shekaru 15 kan kisan abokin kasuwancinsa, ta umarce shi da biyan Naira miliyan 10.