Home » Gwamnatin Kano Ta Ƙaddamar Da Rabon Abincin Buɗa-Baki

Gwamnatin Kano Ta Ƙaddamar Da Rabon Abincin Buɗa-Baki

Mataimakin Gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya ƙaddamar da rabon abincin watan azumin Ramadan na cibiyoyi 91 a faɗin jihar daga  Ƙaramar Hukumar Fagge.

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Daga : Shareep Khaleepha Sharifai

Mataimakin Gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya ƙaddamar da rabon abincin watan azumin Ramadan na cibiyoyi 91 a faɗin jihar daga  Ƙaramar Hukumar Fagge.

Bayanai sun ce gwamnatin jam’iyyar NNPP ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf da ta ƙaddamar da wannan shiri tana da burin raba abincin buɗa-baki ga mabuƙata masu azumtar watan Ramadana.

Gwamnatin ta ce an tanadi cibiyoyi 91 domin raba wa mabuƙata 91,000 abincin buɗa-baki duk rana nan da tsawon kwanaki 27 masu zuwa.

Domin tabbatar da samun nasara, gwamnatin ta ce ta ɗauki masu aikin girke-girke da za su riƙa dafawa sannan su raba wa mabuƙata abincin.

Mataimakin Gwamnan wanda shi ne ke jagorantar shirin raba abincin a bana, ya bayyana gamsuwarsa da yadda aka ƙaddamar da shirin, yana mai kiran waɗanda aka ɗora wa alhakin aikin su tabbatar da raba wa mabuƙata abincin a kan kari.

Aminiya ta ruwaito cewa, Mataimakin Gwamnan ya samu rakiyar wasu ƙusoshin Gwamnatin Kano wajen ƙaddamar da rabon abincin da suka haɗa da Kwamishinan Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Abdullahi Waiya da Kwamishinan Harkokin Addini, Sheikh Tijjani Auwal da sauransu.

Gwamnatin Kano ta jaddada ƙudirinta na rage raɗaɗin al’umma musamman Musulmi a wannan wata mai falala.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?