NOA Ta Yi Watsi Da Kalaman Trump Mai Cike Da Kura-kurai Kan Zargin Yiwa Kiristoci Kisan Kiyashi A Nijeriya.

Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa NOA, ta bayyana kalaman shugaban kasar Amurika Donald Trump, na zargin yi wa kiristoci kisan kiyashi, a Nijeriya nada alaka da kura-kurai da bayanan bogi da hukumar tattara bayanan sirri ta kasar Amurika ta bashi.

Daraktan hukumar Malam Lanre Issa-Onilu, ne ya bayyana hakan, a wajen taron musanta matsayin Nijeriya kan kalaman Trump, da aka gudanar a birnin tarayya Abuja.

Lanre Issa-Onilu ya ce zargin da gwamnatin Amurika ta yi babu kamshin gaskiya ko kadan a cikinsa, kuma wannan tsantsar rashin kyautatawa ce ga Nijeriya.

‘’Issa-Onilu ya ce wannan zargi ba gaskiya ba ne, kuma ba adalci ba ne ga Najeriya, domini ta kan ta Amurka ta san cewa babu wani tsari don  zaluntar Kiristoci a kasar.

A cewarsa, “Maganar cewa ana kisan kiyashi ga Kiristoci a Najeriya ba gaskiya ba ce. Ko Amurka ma ta san haka’’.

Post masu alaƙa

Kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin shekaru 490 ga tsohon shugaban bankin NEXIM.

Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama wanda ake zargi da damfarar mutane da cewa shi babban jami’in Dan sandan ne.

Hisbah ta fara horas da sabbin jami’anta a Jigawa