Gwamnatin Kano za ta fara raba wa ɗalibai mata tallafi
Gwamnatin Kano ta bayyana cewa ta fara shirin raba Naira dubu ashirin ga dalibai mata dubu arba’in da biyar a matsayin tallafi domin ƙarfafa wa iyaye su riƙa tura ‘ya’yansu makaranta.
Gwamnatin Kano ta bayyana cewa ta fara shirin raba Naira dubu ashirin ga dalibai mata dubu arba’in da biyar a matsayin tallafi domin ƙarfafa wa iyaye su riƙa tura ‘ya’yansu makaranta.
Ina farin cikin yi muku jawabi a yau, ranar cikar kasarmu shekaru 63 da samun ‘yancin kai, a matsayina na shugaban kasarmu mai albarka, kuma zallar dan uwanku dan Najeriya.
A yunkurin shugaban kasa na fara daukar matakan sauya tsarin tafiyar da gwamnati domin samar da daidaton tattalin arziki, yaki da hauhawar farashi, bunkasa ayyukan masana’antu, samar da tsaron rayuka da dukiya, da kuma tallafa wa talakawa da sauran mabukata.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa tana aiwatar da shirye-shirye da manufofin da za su bai wa ‘yan kasa damar yaki da kalubalen talauci da aikata laifuka da ta’addanci.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu, zai gabatar da jawabi ga ‘yan Najeriya
Kwamishinan lafiya anan jihar kano Dr. AbubakaR labaran Yusif ya kaddamar da rukakafin cutar mashako wanda aka ansami bullar cutar a wasu kananan hukumumin jahar kano.
Mai alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli a Harkokin Addinin Musulunci, Alhaji Sa’ad Abubakar na uku, ya yi kira ga ƙungiyoyin ƙwadago da su janye batun yajin aiki da zasu shiga a faɗin ƙasar daga ranar Talata 3 ga watan Oktoba.
Gidauniyar Zakka da Wakafi ta Jihar Kaduna ta bayyana cewa, fitar da zakka da kuma bayar da ita ga wadanda addini yace a bai wa sune kadai za su iya magance tsananin talaucin dake addabar jama’a.
Kingiyoyin sun bayyana cewa gwamnatin ba ta aike musu da takardar sanarwar taron ba a kan lokaci Ƙungiyoyin ƙwadagon dai na shirin fara yajin aikin sai baba-ta-gani a faɗin ƙasar nan a ranar, 3 ga watan Oktoba
Gwamnatin jihar Kano ta daukaka ƙara kan hukuncin da wata babbar kotun tarayya ta yanke cewa ta biya diyyar Naira Miliyan Dubu 30 ga wadanda ta rushewa shaguna a filin idi dake unguwar kofar mata.