Tag: Najeriya

Babban Labari Labarai

Sarkin Musulmi Ya Roƙi ‘Yan Najeriya Su Cigaba Da Yiwa Shugabanni Addu’a.

Mai alfarma sarkin Musulmin Najeriya Alhaji Muhammadu Sa‘ad Abubakar na uku ya yi kira ga al’ummar Najeriya su cigaba da saka shugabanni cikin addu’oinsu na yau da kullum. Sultan  ya yi wannan kiran ne a jami’ar Illorin a jiya Alhamis a yayin gabatar da lakcar ƙaddamar da wani littafi domin girmamawa ga farfesa Ishaq Oloyede. […]

Babban Labari Labarai

Matsalar Rashin Tsaro Na Neman Kassara Arewacin Najeriya– Ƙungiyar Tuntuba Ta Arewa

Ƙungiyar Tuntuba Ta Arewa ta ACF, ta nuna damuwarta kan yadda matsalar rashin tsaro ke neman kassara yankin Arewacin Najeriya, Shugaban Kwamitin Amintattun ƙungiyar Alhaji Bashir Muhhamd  Ɗalhatu Wazirin Dutse ne ya bayyana hakan a yayin ziyarar da ƙungiyar takai jihar Borno. Alhaji Bashir Ɗalhatu ya ƙara da cewa yanayin yadda ake samun ƙaruwar tashe-tashen […]

Babban Labari Labarai

Tinubu Ya Naɗa Shugabannin Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yammacin Najeriya

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya naɗa shugabannin sabuwar Hukumar Raya yankin Arewa-maso-yammacin Najeriya. Bola Ahmad Tinubu ya miƙa wa Majalisar Dattawa sunayen shugabannin sabuwar Hukumar Raya Yankin Arewa-maso-yamma domin samun sahalewarsu. Wannan na zuwa ne bayan sanya hannu kan dokar da ta kafa hukumar da shugaban ƙasa ya yi a ranar 24 ga watan […]

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai