Tag: Nigeria

Babban Labari Labarai

EFCC sun gayyace ni – El-Rufai

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai, ya bayyana cewa hukumar EFCC ta aika masa da takardar gayyata zuwa ofishinta, kuma ya amince zai je. Ya bayyana haka ne a wata hira da BBC inda ya ce “Efcc sun rubuto min takadar gayyata zuwa ofishinsu, kuma na amsa musu zan je ranar Litinin mai zuwa” Wannan […]

Babban Labari Labarai

NECO ta saki sakamakon jarrabawar 2025 na dalibai masu zaman kansu

Hukumar Jarrabawa ta Kasa (NECO) ta saki sakamakon jarrabawar dalibai masu zaman kansu na shekarar 2025. Shugaban Hukumar Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi, ya bayyana cewa 93,425 daga cikin daliban sun zana jarrabawar harshen Ingilishi, inda kashi 78.32% (73,167) suka samu akalla Credit. Dalibai 93,330 sun zana jarrabawar Lissafi inda kashi 91.35 % (85,256) suka samu akalla […]

Babban Labari Labarai

An karrama hukumar NOA da lambar yabo

Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Ƙasa, NOA, ƙarƙashin jagorancin Darakta-Janar Malam Lanre Issa Onilu, ta samu Lambar Yabo ta Kwarewa a Gyaran Ɗabi’u da Gina Ƙasa. Cibiyar Centre for Positive Value Reorientation and Advocacy ce ta bayar da lambar yabon a yayin ƙaddamar da littafinta “Paradise at a Crossroads,” a NBA Hall, Ilorin. An […]

Babban Labari Labarai

Sojojin Najeriya sun kashe manyan mayaƙan ISWAP

Dakarun rundunar hadin gwiwa ta Operation Haɗin Kai da ke aiki a yankin arewa maso gabshin Najeriya, sun sanar da nasarar kai wasu munanan hare-hare kan ƙungiyoyin ƴan bindiga da ke addabar yankin. A cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na rundunar, Laftanar Kanar Sani Uba ya fitar, ya ce bayanan sirri sun tabbatar […]

Babban Labari Labarai

’Yansanda sun bankaɗo masu satar katin waya ta intanet

Rundunar ƴansandan Najeriya tare da haɗin gwiwar cibiyar yaƙi da laifukan intanet ta ƙasa (NPF–NCCC) ta bayyana cewa ta bankaɗo wata babbar ƙungiyar masu satar katin waya ta intanet da ta haddasa asarar kuɗi da ta haura naira biliyan 7.7. ’Yan sandan sun ce ƙungiyar na karkatar da katin waya da bayanan intanet na wani […]

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai