Tag: sojoji

Babban Labari Labarai

Sojoji Sun Halaka Yan Boko Haram Shida A Borno

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kisan mayaƙan Boko Haram shida a lokacin da suka daƙile wani hari da mayakan ƙungiyar suka yi yunƙurin kai wa wani sansanin soji a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya. Cikin wata sanarwa da Laftanar Kalan Sani Uba, jami’in hulda da jama’a na rundunar haɗin kai mai […]

Babban Labari Labarai

Rundunar Sojin Nijeriya Ta Yi Nasarar Murkushe Harin Da Boko Haram Ta kai.

Rundunar sojin Najeriya ta ce masu iƙirarin jihadi sun ƙaddamar da hare-hare lokaci ɗaya kan sansanoninta huɗu da ke arewa maso gabashin ƙasar, sai dai ta samu nasarar murƙushe su. Sanarwar da rundunar haɗin gwiwa ta ‘Joint Task Force’ ta fitar a yau Alhamis, tare da sa hannun jami’in yaɗa labaran rundunar Laftanar Kanar Sani […]

Babban Labari Labarai

Sojojin Najeriya Sun Musanta Miƙa Wuyan Bello Turji

Shelkwatar tsaron Najeriya ta musanta rahotanni da ke cewa riƙaƙƙen ɗan fashin dajin nan wanda ya yi ƙaurin suna, Bello Turji ya miƙa wuya ga sojojin ƙasar. Daraktan yaɗa labarai da aikace-aikacen shelkwatar tsaron, Manjo-Janar Markus Kangye ne ya bayyana haka yayin tattaunawa da manema labarai a yau Alhamis. “Maganar ita ce Bello Turji bai […]

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000