Tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido, ya ce shugaba Bola Ahmed Tinubu ya goyi bayan soke zaben shugaban kasa da aka yi ranar 12 ga watan Yunin 1993.
A wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise, Sule Lamido ya ce mahaifiyar Tinubu, Hajiya Mogaji ta jagoranci mata ‘yan kasuwa daga Legas zuwa Abuja domin nuna goyon baya ga shugaban kasar Najeriya a wancan lokacin, Janar Ibrahim Badamssi Babangida.
Lamido ya ce, Tinubu yana bashi dairiya in yana wasu maganganu akan Dimokuradiyya. Musamman in yana kakkausar martani game da yadda shugaban kasa ya soke zaben na 12 ga watan Yuni.
- Yan Sanda Sun Gano Sauran Abubuwan Fashewa 7 A Kano
- Wata Kotu Ta Takaitawa Wani Tela Lokacin Yin Aiki A Kano
Alhaji Sule Lamido ya bayyana cewa, shugaba Tinubu yana majalisar dattawa a matsayin sakataren jam’iyyar SDP, bayan soke zaben na 12 ga Yuni, ya samu tagomashi a fagen siyasar Najeriya yayin da marigayi Janar Sani Abacha ya karbi mulki.
Tsohon gwamnan na Jigawa ya yi ikirarin cewa an kafa National Democratic Coalition (NADECO) ne domin a taya marigayi Janar Sani Abacha yaki ba saboda soke zaben ranar 12 ga watan Yuni ba.