An harbe ɗan bindiga a rukunin gidajen sojoji a Abuja

Sojoji sun harbe wani ɗan bindiga har lahira, bayan gungun ’yan ta’adda sun kai hari da nufin sace wani ɗan kasuwa a rukunin gidajen sojoji na Phase 5 da ke Kurudu a Abuja.  Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 8:47 na dare a ranar Alhamis, lokacin da ’yan bindigar su […]

Read more

Abba kaɗai ke da takarar kai-tsaye a Kano —APC

Jam’iyyar APC ta saya wa Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano fom ɗin neman tazarce babu hamayya a zaɓen shekarar 2027 da ke tafe. Shugabannin Jam’iyyar APC sun ɗauki wannan mataki ne bayan sun rungumi Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Abba a matsayin ’yan takara babu hamayya a kujerar shugaban ƙasa da […]

Read more

Hukumar Alhazai ta ƙasa, NAHCON, ta sanar da cewa za a fara jigilar maniyyatan Najeriya zuwa ƙasa mai tsark daga ranar 3 ga Mayu. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Fatima Sanda Usara, ta fitar a wannan Talatar. A cewarta, jirgi na farko Kamfanin Flynas zai tashi daga Filin […]

Read more

Saudiyya Ta Ba Ɗaliban Najeriya 50 Guraben Karatu A Fannin Man Fetur Da Ma’adinai

Masarautar Saudiyya ta ba wa ɗaliban Najeriya 50 guraben karatu cikakku a fannonin albarkatun man fetur da ma’adinai. Jakadan Saudiyya a Najeriya, Yousef Bin Mohammed Al-Balawi, ya bayyana cewa shirin guraben karatun ya haɗa da kuɗin makaranta, tikitin tafiya, masauki da kuma alawus na wata-wata a Jami’ar  Man Fetur da Ma’adinai ta Sarki Fahd. Jakada […]

Read more