Zauren haɗin kan malamai ya buƙaci gwamnatin Kano ta tsawatarwa ƴan daba da masu saka su.
Zauren haɗin kan malamai da ƙungiyoyin musulinci a faɗin jihar Kano, sun bayyana kaɗuwarsu kan yadda wani taron siyasa ya janyo zubar da jini da kuma rasa rayukan jama’a. Sakataren zauren haɗin kan malaman, Dr. Sa’id Ahmad Dukawa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya raba manema labarai. Haɗakar ƙungiyoyin sun yi […]