Kwalejin sojan ruwa dake Dawakin-Tofa ta kara karfafa hadin gwiwar aiki tare da rundunar yan sandan Kano.

Kwamishinan yan sandan kihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya karɓi bakuncin Kwamandan kwalejin sojan ruwa ta Nijeriya da ke Dawakin-Tofa, Commodore Ahmad Abubakar Madawaki, a hedikwatar rundunar da ke Bompai, Kano. Kwamandan ya ce ya je rundunar ne domin ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin rundunar sojan ruwa da yan sandan Kano, musamman wajen horas […]

Read more

Kwastam ta kama harsasai 3,300 da kayayyakin fasa-ƙwauri a Seme

Hukumar kwastam ta Najeriya ta kama harsasai 3,300 da wasu kayayyakin fasa-ƙwauri da darajarsu ta kai Naira miliyan 365.1 a iyakar Seme. Daga cikin kayayyakin akwai tabar wiwi, magunguna, sigari 310,000, da motoci daban-daban. Haka kuma, jami’an sun kama wata mota da aka bayyana cewa tana ɗauke da kayan abinci, amma aka gano buhunan noodles […]

Read more

Gwamnatin Tarayya za ta biya tsofaffin ma’aikatan da ta sallama shekaru 20 da suka gabata

Gwamnatin Tarayya ta fara tantancewar ƙarshe domin biyan tsofaffin ma’aikatan da aka sallama daga aiki kusan shekaru 20 da suka gabata, bayan wasu daga cikinsu sun yi fama da rashin samun cikakkun haƙƙoƙinsu na tsawon lokaci. Daraktan-Janar na Ofishin Sauye-sauyen Ayyukan Gwamnati (BPSR), Dasuki Arabi Ibrahim, ne ya bayyana hakan a Gombe yayin da yake […]

Read more