Labarai

Rundunar 'yan sanda na shirin janye jami'anta masu yi wa manyan mutane rakiya da tsaro
Babban Labari Labarai

Yan sanda sun harbe ’yan bindiga 4 a Binuwai

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Binuwai, sun kashe wasu ’yan bindiga huɗu bayan sun kai hari wani shingen binciken ’yan sanda a garin Orokam da ke Ƙaramar Hukumar Ogbadigbo. Kakakin rundunar, DSP Udeme Edet, ta ce lamarin ya faru ne ranar Laraba lokacin da jami’an Operation Zenda Joint Task Force ke aiki a shingen. Ta bayyana […]

Babban Labari Labarai

Kotu ta ba Yahaya Bello damar tafiya Umara a watan azumi

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, izinin tafiya Saudiyya domin yin Umara a kwanaki 10 na watan Ramadan mai kamawa. A yayin zaman kotun na ranar Alhamis, alkalin kotun, Mai Shari’a Emeka Nwite ya bayar da umarnin a saki fasfo ɗin tafiya na tsohon gwamnan, wanda yake a […]

Babban Labari Labarai

ECOWAS ta ɗage takunkumin da ta ƙaƙaba wa Guinea

Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afrika wato ECOWAS ta amince da ɗage dukkan sauran takunkuman da ta ƙaƙaba wa ƙasar Guinea bayan kammala miƙa mulki, lamarin da ke nuna cikakken dawowar ƙasar cikin harkokin ƙungiyar yankin. An cimma wannan matsaya ne a yayin taron shugabannin ƙasashe da gwamnatocin ECOWAS da aka gudanar a ƙasar […]

Babban Labari Labarai

’Yansanda sun bankaɗo masu satar katin waya ta intanet

Rundunar ƴansandan Najeriya tare da haɗin gwiwar cibiyar yaƙi da laifukan intanet ta ƙasa (NPF–NCCC) ta bayyana cewa ta bankaɗo wata babbar ƙungiyar masu satar katin waya ta intanet da ta haddasa asarar kuɗi da ta haura naira biliyan 7.7. ’Yan sandan sun ce ƙungiyar na karkatar da katin waya da bayanan intanet na wani […]

Babban Labari Siyasa

NNPP ta soki masu kiran cewa mataimakin gwamnan Kano ya ajiye aiki

Jam’iyyar NNPP ta yi Alla-wadai da kalaman kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Ibrahim Waiya, wanda ya buƙaci mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo ya ajiye aikinsa. Wata sanarwa da kakakin jam’iyyar a jihar Kano, Ibrahim Karaye ya fitar, ya ce har yanzu kundin tsarin mulki ya bai wa mataimakin gwamnan ci gaba da riƙe […]

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai