Tag: Kano

Babban Labari Labarai

Fursunoni 58 Ne Ke Rubuta Jarrabawar NECO A Kano

Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta kasa reshen jihar Kano   ta   sanar   da   cewa   fursunoni   58   ne   suke   rubuta jarabawar NECO a wannan lokaci. Kakakin hukumar Musbahu Kofar Nasarawa ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa daya fitar . Zamu Dauki Mataki Kan Masu Yada Jita-jitar Fadan Daba A Kano- Yan Sanda Sarkin […]

Babban Labari Labarai

Rikicin Cikin Gida Ya Turnuƙe APC A Kano

Wata sabuwar dambarwa ta sake tasowa a cikin gidan jam’iyyar APC a jihar Kano, kwanaki kaɗan bayan saukar Abdullahi Umar Ganduje daga shugabancin APC na ƙasa. Wasu ƴaƴan jam’iyyar sun fito suna neman shugaban APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas wanda na hannun daman Ganduje ne, ya sauka daga muƙaminsa, lamarin da ɓangaren Abdullahi Abbas […]

Babban Labari Labarai

Horon Da Muka Samu A Kasar Amurika Zai Yi Tasiri Wajen Magance Fadan Daba: SP Abdullahi H Kiyawa

  Rundunar yan sandan Nijeriya reshen jihar Kano, ta lashi takobin ci gaba da yaki da masu kwacen waya da harkar daba da sauran miyagun laifuka a fadin jihar. Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan kwanaki kadan bayan daworsa daga wani taro na musamman da ya halatta, […]

Babban Labari Labarai

Jana’izar Aminu Ɗantata: Abba Da Sarki Sanusi Sun Tafi Saudiyya

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf, tare da Gwamnan Jigawa, Umar Namadi da kuma Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, sun tafi ƙasar Saudiyya domin halartar jana’izar Alhaji Aminu Ɗantata. Gwamnan ya jagoranci tafiyar ce domin halarta Sallar Jana’izar a Madina ne, bayan rasuwar hamshaƙin attajirin a birnin Dubai da ke ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a […]

Babban Labari Labarai

Za A Yi Wa Aminu Ɗantata Salatul Ga’ib A Kano

Allah Ya yi wa hamshakin Attajiri, Alhaji Aminu Alhasan Ɗantata rasuwa. Alhaji Aminu Ɗantata ya rasu yana da shekaru 94 bayan fama da rashin lafiya. Ya rasu ya rasu yana da ’ya’ya bakwai da jikoki da dama. Babban sakatarensa, Mustapha Abdullahi Junaid, ne ya sanar da rasuwar a safiyar Asabar. Ɗaya daga cikin attajirai mafiya […]

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai