Yadda Masu Ƙwacen Waya Sun Kashe Ma’aikacin Jami’a A Kano
Masu ƙwacen waya sun kashe wani ma’aikacin Jami’ar Northwest da ke Kano, Buhari Imam, ta hanyar daɓa masa wuƙa a ciki.
Masu ƙwacen waya sun kashe wani ma’aikacin Jami’ar Northwest da ke Kano, Buhari Imam, ta hanyar daɓa masa wuƙa a ciki.
Hukumar kasuwar Singa da ke Kano ta ce za gobe Lahadi ga Yuni, 2025, ba za a gudanar da harkokin kasuwanci ba daga ƙarfe 7 na safe zuwa 7 domin aikin yashe magudanan ruwa.
Mazauna Unguwar Karkasara Babban Giji karamar hukumar Tarauni a Jihar Kano, sun zargi wasu masu dillacin miyagun kwayoyin da yunkurin haifar musu da fitina da kuma kawo cikas ga ci gaban yankin. Gamayyar mutanen unguwar sun koka ne bayan da wasu batagarin matasa suka lalata kayan aikin ginin ofishin Civil Defence da shugabancin karamar hukumar […]
Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da wani kwamitin bincike na musamman da zai duba gobarar da ta tashi a kasuwar wayoyin salula ta GSM da ke Farm Centre, a birnin Kano. Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Umar Farouk Ibrahim ne ya jagoranci kaddamarwar a madadin Gwamnan Kano, inda ya ce kwamitin zai binciki musabbabin gobarar da […]
Hukumomin tsaro a jihar Kano, sun kama wani mutum da ake zargi da yiwa matarsa kisan gilla ta hanyar yin amfani da Wuka ya daba mata a sassan jikinta. Wasu shaidun gani da ido da suka bukaci asakaya sunansu, sun bayyana cewa wanda ake zargin, ya dade yana shan kayan maye, har sai da matarsa […]
A wani bangare na kokarin tabbatar da tsafta da kuma da’a yayin bukukuwan Sallah Babba a jihar Kano, Hukumar Tace Fina-Finai da Dab’i ta Jihar Kano karkashin jagorancin Shugaban Hukumar Abba El-Mustapha, ta bayyana jin dadinta bisa yadda Dakunan Taro da gidajen wasannin a Kano suke bin dokokin ta, a yayin Bikin Babbar Sallah. Kwamitin […]
Rundunar yan sandan jihar Kano, ta gurfanar da mutane 29 a gaban kotun majistiri mai 20 dake zaman ta, a rukunin Kotunan Noman Sland bisa zargin su da aikata laifukan dabam-daban ciki harda zargin kashe Bature yan sandan ƙaramar hukumar Rano CSP Baba Ali. Lauyar gwamnatin jihar Kano, Barista Saima Garba, ta roki kotun ta […]
Rundunar yan sandan jihar Kano, ta tabbatar da gano bindiga kirar AK-47 ta bogi, a gidan daya daga cikin wadanda ake zargi da halaka baturen yan sandan Rano CSP Ali Baba. Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa , ne ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook, inda ya ce an samu […]
Mataimakin babban sufeton yan sandan Nijeriya dake kula da shiya ta daya wato Zone One Kano, AIG Ahmed Garba, ya umarci kwamishinonin yan sandan dake karkashin kulawarsa da su tabbatar da cikakken tsaro a lokacin bukukuwan salla da kuma bayan ta. Kwamishinonin yan sandan da umarnin ya shafa sun hada da na jihar Kano, CP […]
Daga: Zubaida Abubakar Ahmad Gwamnatin Jihar Kano ta bukaci jama’a da su tabbatar da cewa dabbobin da za su yi layya da su ba su dauke da wata cuta kafin Babbar Sallah. Kwamishinan Lafiya na Jihar, Dakta Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, inda ya ce hakan […]