Tag: Kano

Babban Labari Labarai

Majalisar dokokin Kano ta gabatar da ƙudurin tsige mataimakin gwamnan Kano

Majalisar dokokin jihar Kano ta fara shirin tsige mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdulsalam, bisa wasu zarge-zarge da aka gabatar a kansa a gaban majalisar, ranar Alhamis. Shugaban masu rinjaye na majalisar Lawal Hussaini ne ya gabatar da ƙudurin tsige mataimakin gwamnan kan zarge-zarge da suka haɗa da almundahana da kuɗin gwamnati a lokacin da ya […]

Babban Labari Siyasa

An samu ƙarancin masu kaɗa ƙuri’a a zaɓen cike gurbi a Kano

Rahotannin da ke fitowa daga jihar Kano sun nuna cewa an samu ƙarancin fitowar mutane zaɓukan cike gurbin wasu ƴan majalisar dokokin jihar biyu. An gudanar da zaɓukan a rumfunan zaɓe 1,014 a faɗin ƙananan hukumomin Ungogo da Municipal. Bayanai sun nuna cewa duk da isar jami’an zaɓe rumfunan a kan lokaci, da dama mutane […]

Babban Labari Labarai

Gobara ta sake tashi a wata kasuwa a Kano

Wata gobara da ta tashi da asuba ta lalata akalla shaguna 50 a kasuwar Fatima Simra Multi-Purpose Market da ke unguwar Dakata a Jihar Kano. Shugaban kwamitin kashe gobarar kasuwar, Dauda Haruna Chula, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce gobarar ta fara ne misalin ƙarfe 4 na asubahin ranar Juma’a. Ya bayyana cewa […]

Babban Labari Labarai

Hisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a Kano

Hukumar Hisbah a jihar Kano ta ce jami’anta sun kama wasu mutum tara Musulmai a jiya Laraba a take ranar farko ta azumin watan Ramadan saboda an gan su suna cin abinci da tsakar rana. Jihar Kano na da yawan Musulmai, inda tsarin shari’ar Musulunci ke aiki tare da dokokin ƙasa na yau da kullum. […]

Babban Labari Labarai

Kashim Shettima ya isa Kano domin karɓar gwamna Abba zuwa APC

Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya isa jihar Kano domin karɓar gwamnan Abba zuwa jam’iyyar APC, a wani muhimmin taron siyasa da ya ja hankalin jama’a. An shirya taron karɓar gwamnan ne a hukumance a filin wasan Sani Abacha Stadium, inda dubban magoya baya da shugabannin jam’iyya suka fara taruwa tun da wuri. Rahotanni sun […]

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000