Tag: Kano

Babban Labari Labarai

DSS ta kama wanda ya sace yaro dan shekara 5 a Kano

Hukumar  tsaron ta farin kaya (DSS) ta samu nasarar ceto wani yaro mai shekaru biyar, mai suna Muhammad Haruna, daga hannun masu garkuwa da mutane a Kauyen Danzaki, karamar hukumar Gezawa. An gudanar da aikin ceton ne da misalin ƙarfe 7:40 na yamma ranar Alhamis, bayan an sami rahoton cewa an sace yaron kuma masu […]

Babban Labari Labarai

Ƙungiyar mafarauta ta Nijeriya, zata yi zanga-zangar saboda rashin biyan diyya ga iyalan mafarauta da aka Kashe a Uromin Edo

Ƙungiyar mafarauta ta Nijeriya, zata gudanar da zanga-zangar lumana saboda, rashin biyan diyya ga iyalan mafarauta yan asalin jihar Kano, da aka yi wa kisan gilla a Uromin jihar Edo. Akallla mafarauta 16 aka yi wa kisan gilla lokacin da suke hanyarsu ta dawowa gida Kano daga kudancin Nijeriya, lamarin da ya jefa iyalansu cikin […]

Babban Labari Siyasa

APC ta fara faɗawa tarkon rikici a jihar Kano

Kurar rikici ta fara turnuƙewa a jam’iyyar APC mai mulki a jihar Kano, da ke arewacin Najeriya, makonni bayan sauyin sheƙar gwamna Abba Kabir Yusuf. An fara ganin ƙurar ne a tarukan haɗa kan ‘ya’yan jam’iyyar APC tsoffi da sabbi a cikin wasu ƙananan hukumomin jihar. Shugabancin APC ne ya ba da umarnin gudanar da […]

Babban Labari Labarai

Gobara ta tashi a Kasuwar Singa da ke Kano

Gobara ta tashi a Kasuwar Singa da ke birnin Kano a safiyar Litinin ɗin nan. Rahotanni sun nuna cewa ’yan kasuwa da mazauna sun shiga tashin hankali matuƙa sakamakon tashin gobarar a shahararriyar kasuwar kayan abincin kwali da da ke titin Bello Road. ‎An yi asarar dukiyoyi na maƙudan kuɗaɗe a sanadiyyar gobarar ta safiyar […]

Babban Labari Labarai

Wasu matasa sun bankawa ɓarawon waya wuta a Ɗorayi

Wasu matasa a unguwar Dorayi dake jihar Kano sun bankawa wani da ake zargin barawon waya ne wuta, bayan da kwace wayar wata mata. Rahotanni sun ce barawon ya chakawa matar wuka a kirjin ta kafin matasan su hallaka shi ta hanyar kone shi da taya. Tuni aka garzaya da matar zuwa asibiti cikin mummunan yanayi […]

Babban Labari Siyasa

NNPP ta soki masu kiran cewa mataimakin gwamnan Kano ya ajiye aiki

Jam’iyyar NNPP ta yi Alla-wadai da kalaman kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Ibrahim Waiya, wanda ya buƙaci mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo ya ajiye aikinsa. Wata sanarwa da kakakin jam’iyyar a jihar Kano, Ibrahim Karaye ya fitar, ya ce har yanzu kundin tsarin mulki ya bai wa mataimakin gwamnan ci gaba da riƙe […]

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000