Kungiyar Kwadago ta Najeriya ta nuna rashin gamsuwarta da karin farashin man fetur
Kungiyar Kwadago ta ƙasa ta nuna rashin gamsuwar ta da karin farashin man fetur zuwa N617, inda ta ce wannan lamari sam bai wa ƴan najeriya dadi ba.
Kungiyar Kwadago ta ƙasa ta nuna rashin gamsuwar ta da karin farashin man fetur zuwa N617, inda ta ce wannan lamari sam bai wa ƴan najeriya dadi ba.
Shugaban rukunin kamfanin man fetur na ƙasa, Mele Kyari, ya ce yanayin kasuwar man fetur ce tasa farashin man ya ƙaru izuwa Naira 617.
Hukumar da ke sa ido kan harkokin man fetur ta ƙasa ta ce yawan man fetur da ake amfani da shi yau da kullun wanda yake kaiwa lita miliyan 46.38, ya ragu da lita miliyan 65.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya bayar da tabbacin cewar, gwamnatin tarayya a shirye take domin sake duba albashin ma’aikatanta, a wani mataki na rage musu raɗaɗin cire tallafin man fetur.
Biyo bayan cece-kuce da suka da jama’a ke ta faman yi, gwamnatin Tinubu ta umurci sake nazarin shirin bayar da tallafin kudi na Naira 8,000 da nufin samar da agaji ga magidanta masu karamin karfi don rage radadin cire tallafin man fetur.
Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, ya kafa kwamitin kwato kadarorin jihar
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta fara bin diddigin Abdullahi Adamu, shugaban jam’iyyar APC mai mulki na kasa, kan gazawarsa wajen bayyana inda kudade sama da Naira biliyan 32
Hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar nan ya ƙaru zuwa kashi 22.79 a watan Yuni daga kashi 22.41 da yake a watan Maris ɗin shekarar nan.
Farashin Litar Man Fetur ya karu zuwa Naira 617 kamar yadda rahotanni suka bayyana a babban birnin tarayya, Abuja.
Wasu lauyoyi 60 sun garzaya kotu domin shigar da kara na kin sakin Emefiele