Gwamnan Zamfara ya nuna damuwarsa game da hukuncin kotu
A jiya Alhamis kotun ɗaukaka kara da ke zamanta a Abuja ta ayyana zaɓen gwamnan jihar ta Zamfara a matsayin wanda bai kammala ba. inda ta bayar da umarnin sake gudanar da zaɓe kananan hukumomi uku da suka haɗa da Maradun, Birnin-Magaji da Bukkuyum.










