Ana shirin rufe wani katafaren kantin sayayya a Kano
A ranar 14 ga watan Janairun shekara mai zuwa ta 2024 katafaren kantin nan na Shoprite zai rufe reshensa da ke jihar Kano. Yana ɗaya daga cikin manyan kantuna a Najeriya duba da shahararren wurin sayar da kaya na Ado Bayero Mall a nan birnin Kano.










