Gwamnan Bauchi Na Shirin Sauya Sheka Zuwa ADC

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana shirinsa na sauya sheka zuwa Jam’iyyar ADC, inda ya ce jam’iyyar na da damar kalubalantar jam’iyyar APC mai mulki a zaben 2027. Idan Bala Mohammed ya sauya shekar, ADC ta samu gwamna mai ci na farko, wanda hakan zai kara mata karfi a kan tsofaffin gwamnoni da tsofaffin […]

Read more

Gawuna ya koma ADC a hukumance, ya yi rajista a matakin mazaba.

Tsohon mataimakin gwamnan Kano, Nasiru Yusuf Gawuna, ya koma jam’iyyar ADC a hukumance, inda ya kammala rajista tare da karɓar katin zama ɗan jam’iyya a mazabarsa ta Gawuna da ke ƙaramar hukumar Nasarawa a jihar. Jaridar Solacebase ta rawaito cewa Gawuna ya je yin rajistar tare da jagoran tafiyar Kwankwasiyya kuma tsohon ɗan takarar shugaban […]

Read more

Ƴan majalisar wakilai 8 na Kano sun fice daga NNPP zuwa APC

Ƴan Majalisar Wakilai takwas daga Jihar Kano sun sanar da ficewarsu daga jam’iyyar NPP zuwa jam’iyyar APC, lamarin da ya ƙara girgiza siyasar jihar. Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ne ya sanar da sauya sheƙar a hukumance yayin zaman majalisar a yau Talata, bayan karanta wasiƙun da ‘yan majalisar suka aike wa zauren. A cikin […]

Read more

El-Rufai ya sake gurfana a kotun Kaduna

Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya sake gurfana a gaban Babbar Kotun Jihar Kaduna a ranar Talata kan tuhumomin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (ICPC) ta shigar a kansa. An gurfanar da El-rufai ne kan laifuka da suka hada da amfani da mukami ba bisa ka’ida ba, damfara, da bai wa […]

Read more

Sojoji sun ceto mutane 157 da ISWAP ta sace a Borno

Sojojin Rundunar Operation Haɗin Kai sun ceto fararen hula aƙalla 157 da ’yan ta’addan Boko Haram suka sace a kan hanyar Buratai zuwa Kamuya a Jihar Borno. Majiyoyin tsaro sun ce a ranar 30 ga Maris da misalin ƙarfe 2:50 na rana aka kai wa dakarun bataliyar sojoji ta musamman ta 135 da aka tura […]

Read more

Komawar Kwankwaso ADC barazana ce ga APC

Mai fashin baƙi akan al’amuran yau da kullum a Nijeriya, Ibrahim Sadauki Kabara, ya bayyana cewa komawar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, jam’iyar ADC babbar barazana ce ga jam’iyyar APC a Kano dama ƙasa baki ɗaya. Komawar Kwankwaso, wanda shi ne tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, […]

Read more