Labarai

Babban Labari

Ɗan Ganduje Ya Sayi Fom Ɗin Takarar Majalisar Tarayya A NDC

Abdulaziz Umar Ganduje, babban ɗan tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya sayi fom ɗin takarar kujerar Majalisar Tarayya a ƙarƙashin jam’iyyar NDC. Zai tsaya takarar ne a mazaɓar Dawakin Tofa/Tofa/Rimin Gado da ke Jihar Kano. Duk da kasancewar mahaifinsa a jam’iyyar APC, Abdulaziz, ya daɗe yana bin siyasar Kwankwasiyya kuma yana […]

Babban Labari

Hukumar tsaron farin kaya ta Civil Defence  (NSCDC) reshen jihar Gombe, ta kama wasu mutane biyar da ake zargi da hannu a ƙungiyoyin satar babura da na’urorin lantarki a sassa daban-daban na jihar. Kamen ya biyo bayan wasu samame da jami’an hukumar suka gudanar bisa bayanan sirri a ƙananan hukumomin Billiri da Balanga da Akko […]

Babban Labari

Kwamishinan ƴan sandan Kano CP Ibrahim Adamu Bakori ya yaba da haɗin kan da jama’a suke ba su

Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ziyarci yankunan Bichi da Dambatta domin duba halin tsaro da ƙarfafa haɗin kai tsakanin ’yan sanda da al’umma. CP Bakori ya yaba da goyon bayan da jama’a ke bayarwa musamman wajen basu bayanan sirri, inda ya  buƙace su ci gaba da kai rahoton abubuwan da […]

Babban Labari

Daraktan yaɗa labaran DHQ Manjo Janar Samaila Uba, ya bayyana cewa a yaƙin haɗin gwiwa da dakarun Najeriya da kuma sojojin Amurka na AFRICOM suna cin galabar ‘yan ISIS. Manjo Janar Sama’ila Uba ya bayyana hakan ne a jiya Talata a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja.

Siyasa

Barau Ya Zama Ɗan Takarar Sanatan Kano Ta Arewa A APC

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau I. Jibrin, ya zama ɗan takarar Sanatan Kano ta Arewa na jam’iyyar APC mai mulki. An gudanar da taron tabbatar da takararsa a hedikwatar APC da ke Bichi, inda dubban magoya baya daga ƙananan hukumomi 13 na yankin suka halarta. Bayan kammala taron, Barau ya gode wa magoya bayan jam’iyyar […]

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai