Kasuwar Katakon Gombe ta yi gobara na 2 cikin wata ɗaya
Kasuwar Katako ta Gombe ta sake yin mummunar gobara a karo na biyu cikin wata guda. Sabuwar gobarar ta auku ne a daren Litinin, inda ta lalata shaguna da dama tare da dukiyoyi na miliyoyin naira. Rahotanni sun danganta lamarin da matsalar wutar lantarki a kasuwar, wadda kusa da tashar jirgin ƙasa da ke garin Gombe. […]