Kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya ta nemi a janye takunkumin da aka sa wa Nijar
Ƙungiyar dattawan arewacin Najeriya, Arewa Consultative Forum, ta yi kira ga gwamnatin tararraya da ta cire takunkuman da ta sanyawa Nijar, sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasar.