Tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan, Ya Karyata Zargin da Femi Kuti Ya Yi Masa
Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya musanta iƙirarin da Femi Kuti ya yi a kansa, wanda ya ce Hukumar EFCC mai yaƙi da yi wa arziƙin ƙasa ta’annati ta gayyace shi kan zargin sha’anin kuɗi bayan wa’adinsa ya ƙare a matsayin mataimakin gwamnan Jihar Bayelsa.










