Labarai

MALI
Labarai

Kasashen Mali, Burkina Faso, Nijar sun fice daga ECOWAS

Ƙasar Mali a maimakon ƙasashen Burkina Faso da Nijar, ta rubuta wa ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Afirka ta Yamma, wato ECOWAS, takardar sanarwa na ficewa daga ƙungiyar nan take. ƙasashen sun zargi ƙungiyar da sauka daga manufofin da suka assasa kafa ƙungiyar waɗanda ke ƙunshe da aƙidar bunƙasa yankin Afirka. Sannan sun zargi ECOWAS […]

Wannan tabbaci ya fito ne daga bakin kwamishinan ilimin jihar Alhaji Umar
Labarai

Gwamnatin Kano ta jaddada aniyarta ta bunkasa ilimi

Gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin ci gaba da haɓaka ɓangaren Ilimin jihar. Wannan tabbaci ya fito ne daga bakin kwamishinan ilimin jihar Alhaji Umar Haruna Doguwa, wanda yace gwamnatin Kano ba za ta gaza ba wajen bunƙasa ilimi a jihar domin tabbatar da cigaba mai ɗorewa.   Kwamishinan ya bayyana hakan ne a yayin taron […]

KANO-ABUJA
Labarai

Akwai bukatar Naira Tiriliyan 1 domin ƙarasa tin Kano-Abuja

Ministan ayyuka a Najeriya, Sanata David Umahi ya ce kamfanin gine-gine na Julius Berger na neman sama da naira triliyan ɗaya domin kammala aikin babban titin Abuja zuwa Kaduna. Da yake magana a wani taro da daraktocin ma’aikatar ayyuka a Abuja, ministan ya ce farko an ware wa aikin titin Naira miliyan dubu 165 daga bisani aka ƙara kuɗin zuwa naira […]

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano CP Muhammad Usaini Gumel,  ta bakin kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa
Labarai

Kano: Rundunar ‘yan sanda ta kaddamar da rajistar ababen hawa

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano CP Muhammad Usaini Gumel,  ta bakin kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya buƙaci al’ummar jihar da su fara yin rajistar ababensu na hawa ta shafukan intanet ɗin da hukumar ta tanada tare da samun takardun shaidar rajistar.   Wannan na ƙunshe ne a cikin umarnin da Sufeto Janar na […]

Labarai

wasu mata sun fita zanga-zangar lumana a Kano

DAGA: HASSAN ABDU MAI BULAWUS Wasu dandazon mata sun gudanar da zanga-zangar lumana a kan gadar da ke ƙofar Nassarawa domin nuna goyon bayansu ga gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, tare da yin kira ga masu ruwa da tsaki a ɓangaren shari’a kan yin adalci a hukuncin zaɓen gwamnan Kano da ake dakon jiran […]

BAGO
Labarai

Za mu samu Naira tiriliyan 1 daga noma ~Gwamnan Neja

Gwamnan jihar Neja, Umar Bago ya ce gwamnatinsa tana sa ran samun  Naira tiriliyan ɗaya na kudin shiga da za a samu daga Kanfanin Samar da Abinci da Sufuri na Jihar a cikin shekaru biyar masu zuwa. Mashawarci na musamman ga gwamnan kan kafafen yaɗa labarai na zamani, Abdullberqy Ebbo, ne ya bayyana a hakan […]

OPEC
Babu Rukuni

Nijeriya ta jaddada aniyarta ta cigaba da zama mamba a OPEC

Nijeriya ta jaddada aniyarta ta cigaba da zama mamba ta kungiyar ƙasashen masu arziƙin man fetur, OPEC,  inda karamin ministan man fetur Heineken Lokpobiri ya ba da tabbacin cewa ƙasarsa ba za ta gaza ba wajen ci-gaban kungiyar. Ya ce hadin kan kungiyar shi ne yake samar da zaman lafiya da dorewar cinikayya a kasuwar man fetur. […]

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000