Hukumar Hisba Ta Gana da ‘Yan TikTok
A yau ne hukumar Hisba ta Kano, ƙarƙashin jagorancin Kwamandanta, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ta gana da ‘Yan TikTok a hedkwatar hukumar da ke Sharaɗa.
A yau ne hukumar Hisba ta Kano, ƙarƙashin jagorancin Kwamandanta, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ta gana da ‘Yan TikTok a hedkwatar hukumar da ke Sharaɗa.
Allah Ya yi wa Magajin Rafin Hadejia Alhaji Mohammadu Babandede Sarkiki rasuwa, wanda mahaifi ne ga mai MUHASATVR Muhammad Babandede tsohon babban kwanturola na hukumar shigi da fici ta ƙasa.
Shugaban ƙaramar hukumar Honarabul Nasiru Ahmed Kiyawa – wanda ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin – ya ce ‘yan bindigar sun je gidan nasa ne bayan sallar isha’i a ranar Juma’a daddare, inda suka kore mutanen da ke kofar gidan nasa kafin su shiga ciki.
Majalisar Wakilan ƙasar nan ta buƙaci a ƙara yawan kuɗin da aka ware domin ba dalibai rance, wanda a baya aka ware wa miliyan dubu 10.
Gwamnatin tarayya ta kaddamar da kwamiti na musamman da zai samar da motoci masu amfani da Iskar Gas da kuma tashoshi na sayar da isakar gas domin karfafa shirin fara amfani da motoci masu amfani da shi a fadin kasar nan.
Shahararriyar ‘yar fim ɗin Kannywood, Hadiza Aliyu wacce aka fi sani da Hadiza Gabon ta maka wani mai suna Bala Musa a kotun majistare da ke kan hanyar Daura, a jihar Kaduna, inda take zarginsa da lafin ɓata suna.
Sai dai a wannan karon ‘Yan Arewa mazauna kasuwar dabbobi ta Umuchieze da ke ƙaramar hukumar Umunneochi ta jihar Abian sun musanta zargin da gwamnatin jihar ta yi na suna binne gawarwakin mutane a kewayen kasuwar.
Ƙungiyar Ƙwadago ta ƙasa, NLC ta yi kira da a gaggauta ɗaukar matakan daidaita darajar Naira.
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ware duk ranar 29 ga watan Oktoba na kowacce shekara a matsayin ranar tunawa da ciwon shanyewar barin jiki.
Gwamnatin Najeriya ta ce ya kamata a aiwatar da tsarin samar da kasashe biyu masu cin gashin kansu wato kasar Falasdinawa da ta Isra’ila don a tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a yankin Gabas Ta Tsakiya.