Kano: Kwamishinan Shari’a Ya Tabbatar da Takardar Tuhumar Alhassan Ado Doguwa
Antoni Janar kuma kwamishinan shari’a na jihar Kano, Musa Abdullahi Lawan, ya tabbatar da cewa rundunar ƴan sandan jihar ta gabatar da rahoton ta ga ma’aikatar shari’a kan zargin kisan da ake yi wa, Alhassan Doguwa, shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai.










