Labarai

Babban Labari

Mutane sama da 1,000 sun kamu a da cutar Ebola a Congo

Cutar Ebola ta kama sama da mutane dubu daya a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo, yayin da barkewar cutar ta bazu zuwa sansanin ‘yan gudun hijira na uku, sannan ta yi sanadin mutuwar wata yarinya yar kimanin watanni 18. Gwamnatin Kongo ta tabbatar da cewa adadin mutanen da suka mutu ya kai 254. Yaduwar cutar cikin sauri […]

Babban Labari

Ya kamata gwamnatin Najeriya ta rage farashin man fetur – Sheikh Qaribullah

Shugaban ɗarikar Ƙadiriyya na Afirka, Sheikh Qaribullah Sheikh Nasiru Kabara, ya buƙaci gwamnatin Najeriya ta duba yiwuwar rage farashin man fetur domin sauƙaƙa wa al’umma matsin rayuwar da suke fuskanta. Shehin Malamin ya bayyana hakan ne ta bakin wakilinsa, Sheikh Abdulgaffar Nasiru Kabara, wanda ya wakilce shi a taron Qadiriyya Media Connect da aka gudanar […]

Babban Labari

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta karɓi baƙuncin jami’an kwalejin leken Asiri ta Sojojin Nijeriya.

  Rundunar ƴan sandan Jihar Kano ta karɓi baƙuncin jami’an kwalejin leken asiri ta Sojojin Nijeriya da ke Karu a Abuja, a wata ziyara da suka kai hedikwatar rundunar da ke Bompai, domin nazari kan amfani da bayanan sirri wajen dakile rikice-rikice da inganta tsaro. Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan […]

Babban Labari

Fira Ministan Birtaniya ya yi murabus

Fira Ministan Birtaniya, Keir Starmer, ya yi murabus daga mukaminsa bayan matsin lamba da ya karu daga jam’iyyarsa ta Labour. Starmer ya sanar da sauka daga kujerarsa ne a cikin wata sanarwa da aka watsa kai tsaye a talabijin a safiyar Litinin. Ya bayyana cewa ya amince jam’iyyar Labour ba ta ganin shi a matsayin […]

Babban Labari

Kotu ta daure wata mata shekara 2 kan safarar jarirai

Wata Kotun Tarayya da ke Kalaba, Jihar Kuros Riba, ta yanke hukuncin daurin shekara biyu ga wata mata kan laifin safarar yara zuwa ƙasashen waje. Kotun ta tura matar mai suna Asuquo Edem zuwa gidan gyaran hali na tsawon shekara biyu, tare da zaɓi na biyan tara. Hukumar da ke yaƙi da fataucin bil’adama (NAPTIP) ce […]

Babban Labari

Gwamnatin Bauchi ta rufe masallaci saboda rikicin liman da ƴan kwamati

Gwamnatin Jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya ta rufe Masallacin Ibadurrahman da ke unguwar Shingen Abba a cikin garin Bauchi, sakamakon rikicin da ya shafe kusan shekaru uku yana gudana tsakanin kwamitin gudanarwar masallacin da limaminsa. Matakin ya zo ne domin daƙile yiwuwar ɓarkewar rikici da ka iya janyo asarar rayuka a tsakanin […]

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai