Gwamnatin Tarayya Ta Samar Da Shaguna A Hadejia
Shugaban ƙaramar hukumar Hadejia Honarabul Ahmad Abba Ari, ya jagoranci ƙaddamar da buɗe shaguna 6 da hukumar samar da aikin ta Gwamnatin Najeriya (NDE) da haɗin gwiuwa da ƙaramar hukumar suka samar.
Shugaban ƙaramar hukumar Hadejia Honarabul Ahmad Abba Ari, ya jagoranci ƙaddamar da buɗe shaguna 6 da hukumar samar da aikin ta Gwamnatin Najeriya (NDE) da haɗin gwiuwa da ƙaramar hukumar suka samar.
Daga: Muhammad Inuwa Ibrahim Majalisar Masarautar Hadejia a jihar Jigawa ta mika sakon jaje da ta’aziyarta ga iyalan da suka rasa ‘yan uwansu sakamakon matsalar tsaron da ta haifar da kisan gilla a yan kwanakin nan. Da yake jawabi a wani taron hadin gwiwa da al’umomin yankin da abin ya faru Galadiman Hadejia, Alhaji Usman […]
Rundunar yan sandan jihar Jigawa, ta kama wani malamin makaranta da zargin da halaka Almajirinsa mai suna Bashir Ahmed, ta hanyar dukansa da Bulala saboda rashin zuwa makaranta ba tare da sanin malamin ba. kakakin rundunar yan sandan jihar Jigawa SP Lawan Shiisu Adamu, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da aikewa da […]
Gwamnatin jihar Jigawa ta ƙulla ƙawance da kamfanonin samar da dabino na ƙasar Saudiyya da kamfanin Netay Agro-Tech a Najeriya domin bunƙasa noman dabino a jihar.
Cibiyar masana hulda da jama’a ta Najeriya (NIPR) ta yi taron karrama gwamannan jihar Jigawa Malam Umar A. Namadi da lambar yabo mafi girma ta cibiyar (DIAMOND PRIZE) bisa zamowarsa gwarzon gwamna a fannin habbaka aikin noma da samar da abinci.
Rahotanni daga jihar Jigawa na cewa gwamnatin jihar, ta gano ma’aikatan bogi 6,348, yayin tantance ma’aikatan ta.
Mazauna karamar hukumar Jahun a jihar Jigawa na farin cikin dawowar wutar lantarki, bayan shafe shekaru 8 suna cikin duhu.
Gwamnatin jihar Jigawa ta yi alƙawarin taimakawa masana masu bincike akan ciwon ƙoda da ke addabar jama’ar wasu yankuna a jihar.
Tun bayan Iftila’in haɗarin Tankar mai da ya faru a ranar Talata a Majiya dake Jihar Jigawa, zuwa yanzu adadin mutanen da suka rasu sun kai 180 a cewar wasu mazauna yankin. Tun a ranar 15 ga watan Oktoba ne wata babbar tankar dakon man fetur tayi haɗari akan hanyar ta ta zuwa Jihar Yobe […]
Mataimakin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, SP Barau Jibril Maliya ya jajantawa al’ummar Jigawa bisa haɗarin tankar mai da ta yi sanadiyyar rasuwar mutane sama da 95 a Majiya dake ƙaramar hukumar Taura a Jihar Jigawa. Kakakin rundunar yan sandan Jihar, DSP Shaidue Adam ya tabbatar da faruwar lamarin, inda mutane sama da 95 suka rasu, […]