Hukumar kare bayanan sirri ta yi watsi da umarnin CBN kan amfani da bayanan soshiyal midiya
Hukumar kare bayanan sirrin masu amfani da intanet ta ƙasa (NDPC), ta ce umarnin da Babban Bankin Ƙasa (CBN) ya bai wa bankuna na neman bayanan soshiyal midiya na abokan hulɗarsu ya saɓa doka.










