Kano: KACCIMA za ta sanya wa cibiyarta sunan Dangote
Kungiyar ‘Yan Kasuwa, Masana’antu, Ma’adanai, da Noma ta Kano, KACCIMA, ta ce tana shirin sanyawa cibiyar kasuwanci da taro da sunan Shugaban Kamfanin Dangote Group, Aliko Dangote.
Kungiyar ‘Yan Kasuwa, Masana’antu, Ma’adanai, da Noma ta Kano, KACCIMA, ta ce tana shirin sanyawa cibiyar kasuwanci da taro da sunan Shugaban Kamfanin Dangote Group, Aliko Dangote.
Hajiya Aisha Ibrahim Bura ta lashe zaben shugabancin Kungiyar mata ‘yan jarida wato NAWOJ ta kasa, wanda aka gudanar a Birini taraiyya Abuja.
Ƙungiyar da ke yaƙi da safara da bautar da ƙananin yara NACTAL tare da haɗin guiwa da hukumar yaƙi da safarar bil’adama ta ƙasa NAPTIP, da sauran kwamitocin karta kwana da ke yaƙi da wannan ɗabi’a, sun gudanar da taron wuni ɗaya domin wayar da kan al’umma kan matsalolin safar bil’adama da shigi da fici ba bisa ƙa’ida ba a nan jihar Kano.
Kotun ɗaukaka ƙara da ke zaman a babban birnin tarayya Abuja ta bayyana tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna kuma dan takarar APC a matsayin wanda yai nasara a zaben gwamnan jihar Kano da aka gudanar a ranar 18 ga watan maris da ya gabata.
Allah Ya yi wa Mai martaba Ohinoyi na kasar Ebira, Alhaji Ado Ibrahim rasuwa wanda har ila yau shi ne mataimakin shugaban Jama’atu Nasril Islam (JNI) na kasa,
Ƙungiyar ta ce bayan nazari da lissafin da mambobinta suka yi kan yadda suke tafiyar da sana’ar tasu, sun cimma matsayar sanar da sabon farashi inda ta ƙara da cewa abincin kaji mai iganci a yanzu ya haura naira 11,000 a kan ko wanne buhu.
Kano: Wata kotu ta hana a kama Musa Iliyasu Kwankwaso
Gwamnna ya bayyana hakan ne a yayin zaman majalisar zartawas karo na 7 a gidan gwamnati, inda ya yi alƙawarin cewa akwai ayyuka masu yawa da za su zo nan ba da daɗewa ba.
Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta kaddamar da sake dawo da shirin fitar da dalibai kasashen ketare don karo ilimi
Gwamnatin Kano ta raba kayan koyo da koyarwa ga makarantun firamare da sakandire dake fadin jihar nan. Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce samar da kayayyakin zai taimaka kwarai ga makarantun jihar nan domin farfaɗo da su. Kasancewar Inganta ilimi ne abin da Gwamnatinsa ta sa a gaba.